A wani zargi da ministan tsaro Mansur Dan Ali ya yi cewa, akwai wasu manyan sarakunan gargajiya a jihar Zamfara da ke hulda da ƴan bindiga masu kai hare-hare tare garkuwa da mutane.
Wannan zargi ya fusata sarakunan jihar har su ka ƙalubalanci ministan cewa ya fito fili ya bayyana waɗanda ya ke zargi.
Shugaban majalisar sarakunan jihar Zamfara Mai martaba sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmed, ya ce har yanzu su na nan a kan bakan su na ƙalubalantar ministan ya fito ya bayyana sarakunan da yake zargi da mu’amula da ƴan bindiga.
A cewar Sarkin , kamata ya yi ministan ya zo ya ja kunnen sarakunan ko ya faɗi abubuwan da su ka yi, da zai nuna cewa suna da hannu akan lamarin.
Sarkin ya ƙara da cewa idan aka kai su bango za su fasa kwai.

A yanzu dai gwamnatin tarayya ta dakatar da ayyukan haƙo ma’adinai a jihar Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: