Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a JAMB ta bayyana cewa a gobe Litinin ne za ta fara sakin sakamakon jarrabawar da ɗaliban da suka rubuta wanda zai fara daga ranar 29 ga watan Afrilu.
Babban jami’i a hukumar Dr Fabian Benjamin, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Asabar a garin Bwari dake babbar birnin tarayya Abuja.
Benjamin ya kuma bayyana cewa duk a ranar Litinin ne za su fara fitar da sakamakon jarrabawar da daliban suka rubuta, wanda suka fara tun ranar 11 ga watan Afrilu zuwa 18 ga watan.
A cewarsa “Muna nan muna ci gaba da tsare tsaren mu domin fara sakin wannan sakamakon wanda zai kasance cikin wannan satin da zamu shiga,”in ji shi.

“Zamu tura wa kowa nasa sakamakon ta hanyar wayar tarho, wannan sakamakon zai fara fita ne a cikin awa 24 zuwa 48, kamar yadda muka yi shekarun baya. “
“Hukumar ta dakatar da sakin sakamakon ne sabida wasu ɓata gari da ake samu suna karɓar kuɗin mutane da sunan za su taimaka musu, lokacin cire sakamakon da kuma magance waɗanda aka kama da satar amsa lokacin jarrabawar. “
“Duk da haka, hukumar ta sanya matakan tsaro lokacin gudanar da wannan jarrabawar kamar irin su CCTB domin tabbatar da cewa daliban sun kula da abinda suke yi. “
Zamu saki Sakamakon,ne ta hanyar gajeren saƙo (SMS) wannan sabon tsari ne da zai sauƙaƙewa ɗalibai duba sakamakon nasu ba sai sun je wurin duba saka mako ba, ko sun ɓata kuɗin su a yanar gizo ba “
Daga karshe ya buƙaci ɗliban da su yi watsi da duk saƙonnin jita-jitar da wasu suke yaɗawa a kan sakin sakamakon, wanda hukumar JAMB ta nesanta kanta da hakan.

