Tare da Zainab Sani Usman

A  cigaba da kawo muku kayatattun  sinadaran kayan gyaran  jiki  a yau shafin naku na mata adon gari zai cigaba da kawo muku sinadarin da zakuyi  amfani dashi don gyaran gashin mu.

Kamar yadda a lokacin sanyi muka dage wajen kula da gashinmu to haka ma a yanzu zamu dage wajen kula dashi domin kuwa idan muka ce zamu tsaya to lalle zamu zama abin kyamata dan duk wadanda suke makusantanmu zasu dinga jin irin tashin tsamin da gashin zai dinga yi, wasu zasu iya fadamaka wasu kuwa suna jin nauyin su ce kanka yana tsami ko wari.

Wannan tasa naga ya dace mu dage mu kula da kanmu kuma a lokacin nan na zafi ma kanka damunka zai yi gashin idan ba’ayi kitso ba.

HADI NA DAYA.

1, Man Zaitun

2, habbatussauda

3, kwanduwar kwai

A samu kwanduwar kwai  banda ruwan, a hada da cokali  daya na habbatussauda, cokali daya na man zaitun a hada su guri guda, bayan sun hada jikinsu sosai a shafa a kai sosai ko’ina  yaji da yamma za’a shafa idan gari yaw aye sai a wanke da ruwa mai dumi, idan ya fita tas ya bushe  a shafa mai dai dai misali ayi kitso akalla dai duk sai sati ya kamata a dinga yin kitson kuma duk yi a wanke kan kafin yin kitson.

HADI NA BIYU

1, Man zogale

2, man zaitun

3, man kwakwa

4, man alayyadi

Shi kuma wannan hadin kullum za’a dunga shafawa a gashi idan an fito da ga wanka, idan kitso ne akan mutum sai a dinga  bin layin kitson ana shafawa idan kuma kan a tsefe yake sai a dinga tsaga gashin da kibiya ana shafawa har a gama.

HADI NA UKU

1, Ganyen Magarya

2, Man Zogale

3, kanun fari kadan

A daka ganyen magarya a hada da man zogale da kanun farin kadan  a dinga shafa wa gashi shima wannan hadin yana gyara gashi sosai.

Haka kuma kamar yadda na fada a baya yawaita cin wadannan kayannan yana kara kaurin gashi da yawansa sannan kuma gashin yayi baki.

1, Cukwui

2, Man zaitun

3, Cucumber

4, Man shanu

Da fatan zamu cigaba da dagewa muna gwada dukkan abubuwan da muke kawowa.

Muna fatan zaku cigaba da bibiyar mu don kawo muku kayatattun sinadaran kayan gyaran jiki.

Allah ya sa da mu da Albarkar wannan wata da yake tunkaro mu na Ramadan  amin summa amin.

 

One thought on “Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari”
  1. Hello. I have checked your matashiya.com and i see you’ve got some duplicate content so probably it is the reason that you don’t rank high in google.
    But you can fix this issue fast. There is a tool that creates articles like human, just search in google: miftolo’s tools

Leave a Reply

%d bloggers like this: