Connect with us

Labarai

Sai da ƴan sanda suka mana fyaɗe bayan da suka kamamu – Karuwan da aka kama a Abuja

Published

on

“Bayan sun kamamu suka buƙaci mu basu kuɗi sabpda bamu da kuɗi ya sa suka mana fyaɗe.
Wasu daga cikin ƴan sandan sun yi amfani da lefar fiyawata a matsayin ledar kariya wasu kuwa a haka suka yi amfani da mu” Inji ɗaya daga cikinsu.
Ƴan matan dai an kamasu ne yayin da suke cin duniyarsu da tsinke a mabambanran godan rawa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Matan da aka kama sun haura 60 daga samamen da ƴan sanda suka kai.
A cewar wata daga cikinsu ta bayyanawa kotu cewar, an yi musu fyaɗen ne a gefen wata makarantar koyon yaƙi a Abuja, ta ce mutum biyu ne suka haike mata sannan kuma suka kaisu caji ofis gar aka kawosu kotu.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Gwamnatin Borno Za Ta Dinga Biyan Daliban Jinya Da Ungozoma 30,000 Duk Wata

Published

on

Gwanatin jihar Borno ta sanar da fara biyan daliban jinya da ungozoma tallafin karatu ga kowanne dalibi har N30,000 duk wata a fadin jihar.

 

Gwamna Babagana Umara Zulum ya tabbatar da lamarin jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu yayin bikin kaddamar da tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin Borno a Maiduguri, babban birnin jihar.

 

A cewar jaridar Daily Trust, gwamnan ya tabbatar da cewa dalibai 997 da suka fito daga jihar ne zasu mori tallafin.

 

Ya kara da cewa tallafin an yi shi ne ga daliban lafiya domin karfafa musu guiwa da samar da wadatattun ma’aikatan lafiya a jihar.

 

Jawabin nasa ya nuna gwamantin za ta kashe jimillar N1.3b a kan daliban a matsayin tallafi.

 

Mai girma gwamnan ya kuma bayyana cewa tallafin ya shafi kudin makaranta da alawus da za a rinka basu duk wata.

 

A cewar gwamnatin, daliban zasu rinka karban alawus din ne daga shekarar da suka fara karatu har su kammala.

 

Gwamnan kuma ya yi alkawarin bada aiki nan take ga dukkan daliban da suka nuna bajinta a lokacin karatun nasu.

Continue Reading

Labarai

NDLEA Ta Lalata Haramtattun kwayoyin A Legas Da Osun

Published

on

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta yi nasarar lalata haramtattun kwayoyi a jihohin Legas da Ogun.

Hukumar ta samu nasarar ne a ranar Talata, 16 ga watan Afrilu.

A cikin sanarwar da hukumar ta fitar a shafinta na Facebook, ta tabbatar da lalata jimillar kilogiram 304,436 da kuma lita 40,042 na haramtattun kwayoyi da ta kama daga sassan jihohin Legas da Ogun.

Hukumar ta lalata haramtattun kwayoyin ne da ta kama a bainar jama’a a Badagry da ke jihar Legas.

Shugaban hukumar ta kasa, Mohamed Buba Marwa ya ce lalata haramtattun kwayoyi da aka kama ya biyo bayan umarnin kotu ne.

Buba Marwa ya yi kira domin samun karin goyon bayan jama’a kan kokarin da hukumar NDLEA da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da yi na dakile matsalar shan da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Marwa ya kara da cewa kwayoyin da suka kama nau’o’i ne daban-daban da suka hada da koken, kanabis da tramol.

Shugaban ya kuma mika godiyarsa ga sarakunan gargajiya, shugabannin tsaro, malamai, kungiyoyi da sauran wadanda suka shaida lalata kwayoyin.

Continue Reading

Labarai

Babbar Kotun Tarayya Ta Jingine Dakatarwar Da Aka Yiwa Ganduje

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya samu nasara a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano.

 

Babbar kotun ta jingine dakatarwar da shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, suka yi wa tsohon gwamnan na Kano.

 

Alƙalin kotun, mai shari’a Abdullahi Liman ya umurci shugabannin APC na mazaɓar Ganduje, kada su yi aiki da umurnin babbar kotun jihar na dakatar da Abdullahi Umar Ganduje.

 

Mai shari’a Abdullahi ya kuma ya hana duk waɗanda umurnin babbar kotun jihar ya shafa bin umurnin, har sai an saurari ƙarar da Ganduje ya shigar ta neman a yi masa adalci a saurari ɓangarensa.

 

Wannan umurnin dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan babbar kotun jihar ta amince da buƙatar shugabannin APC na mazaɓar Ganduje ta dakatar da tsohon gwamnan na Kano.

 

Shugabannin dai sun dakatar da Ganduje ne saboda zargin cin hanci da rashawa da almundahana da gwamnatin jihar Kano ke yi masa.

 

Kotun ta kuma sanya ranar 30 watan Afrilu domin sauraren buƙatar da Abdullahi Umar Ganduje wacce lauyansa Jazuli Mustapha ya gabatar a gabanta.

 

Waɗanda ake ƙara a cikin ƙarar sun haɗa da Haladu Gwanjo, Nalami Mai AC, Muhammadu Baiti, Danmalam Gata, Musa Lado, Laminu Sani Barguna, Umar Sanda, Auwalu Galadima da Abubakar Daudu. Sauran sun haɗa da rundunar ƴan sandan Najeriya, kwamishinan ƴan sandan Kano, hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), da hukumar kare farar hula (NSCDC)

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: