A wani labari da mujallar matashiya ta samu daga Real Madrid na nuni da cewa ƴan wasan Madrid da dama basa goyon bayan zuwan ɗan wasan Manchester United Paul Pogba, wanda ake sa ran ƙungiyar za ta saya a ƙarshen kakar wasa ta bana.
Pogba na cikin manyan ƴan wasan da mai horar da Real Madrid Zinaden Zidane ke fatan saya a ba na,saboda irin matsayin da ta ta fuskanta ta koma baya matuka a ƙarshen kakar wasa ta bana.
Shi kuwa pogba ya bayyana a shirye yake ya sauya ƙungiya zuwa Madrid ƙarƙashin jagorancin Zidane
Sai dai a ɓangare guda ƴan wasan Real Madrid sun nuna rashin amincewa da zuwan pogba inda suka ce, zuwan ɗan wasan Chelsea Eden Hazard cikinsu, shi zai fi taimakawa matuka wajen samun nasarori, amaimakon pogba,mafi akasarinsu basu gamsu da ƙwarewar Pogba, dan haka suke ganin zuwansa bashi da amfani.