Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta tabbatar da cafke muhammad Hamza mai shekaru 72 tare da Kamisu Muhammad a filin jirgin sama na Aminu kano, dake jihar kano.

Kwamandan hukumar dake filin jirgin sama Ambrose Omuru ne ya tabbatar wa manema labarai cewa, sun cafke Muhammad Hamza ne da Kamisu hamza tun 24 ga watan Afrilu,suna ƙoƙarin zuwa ƙasar saudiya da wasu kwayoyi a cikin jakunkunan su.

Kwamandan ya bayyana cewa wanda ake zargi ɗan wani ƙauyen Gwaranduma ne dake ƙaramar hukumar Daura a jihar Katsina.

Ambrose ya kuma tabbatar da cewa sun taɓa kama shi a shekarar da ta gabata yana yuƙurin sakawa wasu mata biyu kwayoyi a jikin jakunkunansu.

Wanda ake zargi duk sun musanta zargin don haka bayan an gama bincike zasu gurfanar dasu a kuliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: