Ministan lafiya, Farfesa Isaac Adewole, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda likitoci ƴan Najeriya ke ficewa daga ƙasar suna komawa wasu ƙasashen don neman kuɗi.
Wannan dalili ka iya jawo matsala wajen daƙile matsalar kiwon lafiya a najeriya kasancewar likitoci suna fifita kuɗi sama da aikinsu.

ministan lafiyar Najeriya, Farfesa Isaac, ya bayyana takaicinsa bisa hatsarin da ke cikin ficewa da likitoci ƴan asalin Najeriya suke yi zuwa wasu ƙasashen su yi aiki.
Inda yace wannan lamarin zai kawo naƙasu wajen cigaban samar da kiwon lafiya ingantacce a Najeriya, musamman yara da mata.
Ministan ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban asibitin koyarwa ta Alex Ekwueme da ke Abakaliki, Dakta Emeka Onwe, wanda ya wakilici ministan a wajen taron shekara-shekara na kungiyar likitoci ta kasa.
Wannan lamari ba iya likitoci bane ke hanƙoron ficewa daga ƙasa ba don neman kuɗi hatta ɗaiɗaikun mutane kowa burinsa ya samu damar da zai fice daga Najeriya don neman arziki, duk da ɗumbin Arzikin da najeriya take dashi.

