Hotuna
Hotunan Ahadiza Gabon na rabon kayan abincin azumi ga mabuƙata
Hotuna
Hotunan yadda Buhari ya gabatar da kasafin kuɗi
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayin da yake gabatar da kasafin kuɗi
Ƴan majalisar dokokin Najeriya yayin da suke sauraron bayanin shugaban ƙasa
Hotuna
Bayan shekaru 10 yana waƙa, a karon farko ya saki bidiyon waƙar sa ya fito a ciki
Abdul D One mawaƙin da ake damawa da shi a masana antar fina finai ta Kannywood ya saƙi waƙa ta farko da ya fito a faifan bidoyo mai auna KECE TAWA.
Mawaƙin da ya bayyanawa Mujallar Matashiya cewar, a tsawon shekaru 10 da yayi yana waƙa bai taɓa fita a faifan bidiyo ba sai a yanzu.
Asalin sunansa Abdulƙadir Tajudden wanda aka haifeshi a garin Dikke da ke ƙaramar hukumar Funtua a jihar Katsina.
An haifeshi a ranar 26 ga watan satumba na shekarar 1994.
Ya zauna a ƙarƙashin kamfanin Shareef Studio da ke ƙarƙashin jagoranci da kulawar mawaƙi Umar M Shareef.
Duk da kasancewar mawaƙin yana garin Kaduna don cigaba da gudanar da sana arsa ta waƙa.
Waƙoƙinsa sun yi shura kuma ana sakasu a fina finai da dama, wasu kuma kan bashi aikin waƙa don su fito a cikin bidiyon.
Duk da kasancewarsa mawaƙi mai ƙaramin shekaru idan aka kwatanta da sauran manyan mawaƙa da ludayinsu ke kan dawo, Abdul D. One ya shahara wanda ya samu lambobin yabo da dama a kan waƙoƙinsa.
Ya kan yi waƙoƙin da suka danganci yanayi musamman waƙarsa ta kwananan wanda ya yi a kan rashin tsaro a Najeriya.
Ko da Mujallar Matashiya ta tambayeshi ya yaji bayan da ya saki wannan bidiyon waƙarsa ta farko a shafinsa na Youtube?
Abdul D One ya ce ya ji daɗi ga yadda aikin ya kasance kuma ya samu yabo da yawa daga mutane daban daban a kan waƙar.
Wasu daga cikin waƙoƙinsa waɗanda suka shahara akwai :-
1 Mahaifiya
2 Kar ki manta da ni
3 Dakta Bahijja
4 Abokiyar Rayuwa wanda Adam Zango ya fito shi da jaruma Zee Fretty.
5 Jaruma a cikin fim ɗin Jaruma.
6 Nawwara
7 Shaƙuwa
8 Baya ba zani
9 Waƙar biki ta gidan biki wato Ga Amarya
10 Abinda yake Raina wanda aka saka a fim ɗin mansoor
Hotuna
Hotuna – Taron tsofaffin ɗalibai aji na 1998
Taron tsofaffin ɗalibai aji na shekarar 1998, wanda suka yi a kwalejin shari a ta jihar Kano wato Legal a yau.
-
Labarai8 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari