Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Mu shaƙata

Tun da nake Ban Taɓa yin Zina ba, kuma bazan yi ba da yardar Allah— Nafisa

Jarumar Fina finan Hausa ta “Kanywood” NAFISA ABDULLAHI ta kare kanta Kan zargin da mutane ke yiwa Masu Sana’ar Fina finan Hausa cewa Mutanen banza ne.
Nafisa ta kare kanta da cewa ba ruwanta da kudin kowa, Domin basa Burgeta,a cewar ta da kuɗi zasu ruɗeta to da batakai matakin da take a yanzu ba, tsakaninta da mutanen da suke mu’amala sai dai Soyayya ta Gaskiya.
Nafisa ta bayyanawa Mujallar Fina finai ta “Kanywood” Cewar masu kudi da dama ne suke son yin lalata da ita domin su kaita Su baro ta amma taƙi Amincewa,dasu,
Nafisa tace kuɗi basa Ruɗarta har idan banata bane,
Jama’a dai da dama nayiwa Jaruman fina finan hausa Kallon Mutanen banza da suke Gurɓata Tarbiyar Mutane sai dai ba a taru an zama ɗaya ba a cewar Nafisa.
Nafisa Abdullahi ta ƙara da cewa masu nuna maita da naci a kants Sai dai su haƙura, babu wanda zai kusanceta face Mijinta Wannan Shine Alƙawarin da ɗaukar wa kaina.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: