An tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan na shekarar 1440 wanda ya yi dai dai da shekarar 2019 miladiyya.

Mai alfarma sarkin musulmi alhaji Abubakar sa ad lll ne ya bayyana hakan bayan samun rahoton ganin jinjirin wata da aka yi a sassan jihohin Najeriya.

An da watan azumin ne a jihohin da auka haɗa da Sokoto, Borno, Yola Kano da sauransu.

Tuni dai dama ƙasar Saudiyya ta bayyana ganin watan tun tuni wanda a halin yanzu suke daf da fara sahur ɗin azumin farko da shekarar 1440 kamar yadda wani ya bayyanawa Mujallar Matashiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: