Wani mai kiwon kaji da samar da kwai a jihar Kano ya bayyana cewar a shekarar azumin bana kwai zai yi ƙaranci musamman ma ga masu siya na gida.

Hakan ya faru ne sanadin zafi da yake sanadiyyar mutuwar kaji masu yawa a kullum.
Muhammad Aminu Adamu ya bayyanawa mujallar Matashiya cewar, yanayin zafin da ake fuskanta a bana ya haura tanadin da sukewa kajin don gujewa afkuwar mutuwarsu ko kuma ƙarancin kwan da suke yi.

Ya bayyana cewar suna iya bakin ƙoƙarinsu don ganin sun bawa kajin rigakafi tare da kaucewa dukkan abin da zai faru a da su sanadin zafin

” Idan ana zafi mai yawa kaji suna mutuwa, bs sa cin abinci sannan kuma ba za su na yin kwai kamar yadda suke yi a yanayin damina ko sanyi ba.
Akwai barazanar ƙarancin kwai a azumin bana da kuma hauhawar farashinsa a kasuwanni.