A yau litunin da ya yi dai dai da 1 ga watan Ramadan musulmi a faɗin Najeriya sun fara Azumin watan Ramadan.

Tun bayan sanarwar sarkin musulmi na cewar an samu sanarwar ganin wata a wasu daga cikin jihohin Najeriya.

Sai dai wani al amari da kw ciwa al umma tuwo a ƙwarya yadda ƴan kasuwa ke tsawwalawa a kayan ci ko sha a lokacin azumi.

Duk da cewa akwai ƙalilan da ke sauƙaƙawa cikin kasuwancin nasu, amma hakan ba ya wadatar da mabuƙata.

Mujallar Matashiya na kira ga dukkanin mai wata dama da zai iya sauƙaƙawa al umma da ya duƙufa don samun dacewa a ranar alƙiyama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: