Gwamnan kano Dr Abdullahi umar Ganduje, ya bayyana aniyarsa ta yi wa hukumar Hisbah Garanbawul sakamakon yadda hukumar ta gurɓata daga doran addini yadda aka ɗorata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin taron auren zauwara 1500, da gwamnatinsa tayi a ranar lahadi.
Ganduje ya bayyana cewa ba abin da ke a hukumar face danne haƙƙi Da daƙile ma’aikata da kuma ci da addini da shugaban hukumar yake.
A sabo da haka dole mu chanza wannan al’amari da ake ta hanyar naɗa mai kishin addini kuma matashi mai jini a jika ba mai ci da addini ba.

Idan ba’a manta ba tun a watannin baya a gaje hukumar Hisbah aka garƙame kofan shugaban hukumar Malam Mohammad Aminu Ibrahim A Daurawa tare d fito masa da littatafansa a lokacin ya tafi Saudiya don yin Umara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: