Tare da Abdurrahman Ibrahim Zage

Ibada ko bautar Allah (SAW) ya k’unshi dukkan maganganu da aiyukan bayi na zahiri da badininsu, wad’anda Allah Ta’ala ya yarda a bauta masa da su.
Domin bautarsa ita ce manufar samar da halittu gaba daya…
Ita wannan manufa ta kan kasance mafi tsada da girman falala, a cikin wannan wata mai afarma,,, mai yawan fa’ida da madaukakiyar makoma ga muminai..
A cikinsa ne Allah ya saukar da tsarkakakken zancensa (Alqur’ani) ya shimfida kyaututtukan gafara da falalarsa ga bayinsa, tare da ninka ladan aiyukan alkhairin su. Allah Ta’ala ya ce: ” Watan Ramadan wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa shiriya ga mutane “.
Imamud-Dabariy ya rawaito hadisi daga Annabi (S) ya ce: “an saukar da littattafan Ibrahim (AS) a daren farko na Ramadan, aka saukar da Attaura a daren shida ga Ramadan, kuma aka saukar da Injila a daren sha uku ga Ramadan, sannan aka saukar da Alqur’ani a daren ashirin da hudu ga Ramadan”.

Haka zalika Allah Ta’ala ya sanya Ramadan ya zamanto ruwan wanke dukkan daud’ar zunubai, tunatarwa ga gafalalle, makarantar ilmantar da jahilai, kwad’aitarwa ga ma’abota aikata aikin alkhairi.
Dama ce ga wanda ya banzatar da kansa cikin kangarewa mahaliccinsa a watannin da suka gabata, da zai sabunta imaninsa ta hanyar tuba da komawa ga Allah..
Allah Ta’ala ya kirayi bayinsa gaba daya, da su tuba daga dukkan zunubansu.. yana cewa: ” ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku muminai don ku rabauta”.
Wannan kira ne da yake da alaqa da sauran watanni,,, amma mafi dacewar lokacin da ya kamata bayi su shagalta da tuba ga Allah shine Ramadan,, saboda baiwar keb’antattun falaloli da Allah yayi masa, wad’anda suke ishara zuwa ga albarkarsa da girman sha’aninsa..
Imam Ahmad da Nisa’i sun rawaito hadisi daga Abi Huraira (R) ya ce: yayin da Ramadan ya gabato, sai Annabi (S) ya ce; “hakika Ramadan zai zo muku, wata mai albarka, Allah ya wajabta muku yin azumi a cikinsa, ana bude kofofin Aljannah, kuma a rufe kofofin Jahannama a cikinsa, sannan ana daure Shaidanu, a cikinsa akwai daren Lailatul-kadri mafi alkhairi daga kwanaki dubu, duk wanda aka haramta masa alkhairin sa hakika an haramta masa (dukkan alkhairai).

Leave a Reply

%d bloggers like this: