Connect with us

Labaran jiha

Gwamna Ganduje Ya Yi Alkawarin Rattaba Hannu Ga Sabuwar Dokar Kirkirar Sababbin Masarautu A Jihar Kano

Published

on

 

Daga Abba Anwar

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi alkawarin rattaba hannu ba tare da bata lokaci ba, ga kudurin nan da Majalisar Dokoki ta Jihar za ta turo masa kan bukatar samar da wasu sababbin Masarautu guda hudu daga masarautar Kano.

Ya bayyana hakan ne a yau Laraba a jawabi ga ‘yan jarida daf da fara zaman Majalisar Zartaswa ta jiha, a karo na 136, a gidan gwamnatin jihar Kano.

Ya ce sun samu labarin wata kungiya wadda ya bayyana da masu kishin jihar Kano, su ka kai bukatarsu ga Majalisar Jiha kan kara kirkiro wasu masarautu daga wadda a ke da ita yanzu.

Sai ya ce “A shirye nake da na rattaba hannu a wannan Kuduri da zarar Majalisa sun turo min ba tare da bata lokaci ba.” Masarautun da a ke bukatar kirkirowa kuwa sune, a Rano, Karaye, Bichi da Gaya.

Ya kara da kalubalen cewa ai duk mutumin da ya zo da wannan irin bukata an tabbatar ya na da tsananin kishin jama’ar jihar Kano din ne. Da kuma jihar gaba dayanta, kamar yadda ya nuna.

“Da zarar Majalisa ta gama yin duk abubuwan da za ta yi a kan wannan kuduri, kuma su ka kawo min, to ina mai tabbatarwa da al’umma cewar zan sa hannu kudurin ya zama Doka nan take ba tare da bata wani lokaci ba,” ya ce.

Sannan kuma ya tunasar da cewa dama ai tuntuni shekaru da yawan gaske da su ka wuce an so a samar da wasu masarautun daga cikin masarautar jihar Kano, amma Allah bai yi ba.

A dalilin haka ya ce sai yanzu Allah Ya kawo lokacin da wannan abu zai tabbata. “Ba za mu bata lokaci ba kuwa wajen tabbatuwar wannan aikin na ci gaba,” ya kara tabbatarwa.

Ya kara da cewa ya dau aniyar sa wa kudurin hannu ne ya zama doka, musamman ma saboda wannan wani abin alheri na wanda jama’ar Kano su ke maraba da shi. Kuma hakan a cewarsa zai kara samar da ci gaba mai dorewa ga wannan jiha.

“Akwai tabbacin za a samu ci gaba na gaske a dukkanin bangarorin wannan jiha ta mu mai albarka. Fatanmu ma shi ne kar abin ya ja wani lokaci,” in ji Gandujen.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Masarautar Gaya Ta Tuɓe Dagacin Gudduba Bisa Badaƙalar Filaye

Published

on

Majalisar masarautar Gaya ta tuɓe Dagaci ƙauyen Gudduba da ke yankin ƙaramar hukumar Ajingi Mallam Usman Muhd Lawan.

Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na masarautar Malam Aminu Ahmad Rano ya fitar da tsakar ranar yau Laraba.

Sanarwar ta ce, Sarkin Gaya Dr Aliyu Ibrahim Abdulkadir wanda ya sanar da hakan ya ce bayan dogon bincike an samu Dagacin da hannu dumu-dumu wajen badaƙalar filaye.

Haka kuma sanarwar ta kuma umarci Madakin Gaya Alhaji Wada Aliyu da ya tura wakilin da zai kula da harkokin shugabancin kauyen.

Masarautar ta ƙara da cewa ba za ta saurara kan duk wani rashin adalci ko aikata wani abu da zai taɓa mutunci al’umma ko kuma masarautar ba daga masu riƙe da sarautun gargajiya.

Continue Reading

Labaran jiha

Ɗanzago Ya Sake Maka Abdullahi Abbas Shugaban APC na Kano A Kotu

Published

on

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A.M Liman a ranar Talata, ta ƙi amincewa da sauraron ƙarar da Ahmadu Haruna Ɗanzago ya shigar na neman a shigar da ƙarar Abdullahi Abbas kan hana Abdullahi Abbas bayyana kansa a matsayin Shugaban APC na Kano.

Ɗanzago ta hanyar sammacin da ya samo asali, ya bayyana cewa shi ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne mai rijista a Kano.

Ya ci gaba da cewa a ranar 16 ga Oktoba, 2021 ne aka zaɓe shi bisa ƙa’ida a matsayin shugaba, yana mai cewa Abdullahi Abbas (wanda ake kira na daya) a halin yanzu yana riƙe da muƙamin da ake zargin shi ne shugaban jam’iyyar, inda ya ce ya tsaya takarar ne ba tare da ya ajiye mukaminsa na riƙo ba. Kwamitin jam’iyyar, kafin ya yi takara a matsayin mai mahimmanci.

Tun da farko, lauyan waɗanda ake ƙara Cif MN Duru, ya buƙaci kotun da ta yi watsi da ƙarar saboda rashin iya aiki da kuma motsa jiki kawai.

A wata takardar rantsuwa da sakataren jam’iyyar APC na Kano, Ibrahim Sarina ya yi, ya roƙi kotun da ta fara sasanta batun shari’ar da kotun ta ke domin ya zama hanyar yanke hukunci.

A hukuncin da ya yanke kan ƙin amincewar farko, Mai shari’a Liman ya ce.

“Na yi amfani da takardun shari’a da lauyoyin biyu suka gabatar na yi imani da cewa sashe na 251(1) na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 kamar yadda aka yi wa kwaskwarima, ya bayyana ƙarara a gaban wata babbar kotun tarayya.”

Ya ci gaba da cewa, “Kamar a misali, hukumar INEC, wadda ita ce mai kulawa da alkalan majalisar da aka gudanar, ya zama dole a shiga a matsayin jam’iyya a wannan ƙara,” inji shi.

Mai shari’a Liman ya ci gaba da cewa babbar kotun tarayya na da hurumin sauraron duk wani ƙara da hukumar gwamnatin tarayya ta shiga a matsayin jam’iyya.

Ya jaddada cewa babu inda aka fara gabatar da ƙarar da mai shigar da ƙara ya bayyana INEC a matsayin jam’iyyar da ta kai ƙara a shari’ar.

Ya kuma bayyana cewa ƙarar da mai shigar da ƙarar bai shiga cikin sashe na 251(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 kamar yadda aka gyara ba.

Ya ce rashin shiga hukumar ta INEC kamar yadda ya dace a cikin ƙarar, ya hana kotun sauraron ƙarar.

Alkalin da ke jagorantar shari’ar, saboda haka, ya fitar da ƙarar don rashin hukumci.

Da yake magana da manema labarai bayan yanke hukuncin, Cif MN Duru ya bayyana farin cikinsa.

A nasa bangaren, lauyan wanda ya shigar da ƙara, Barista Solomon ya ce za su fara nazarin hukuncin, kuma za su shawarci mai ƙara yadda ya kamata.

Continue Reading

Labaran jiha

An Gano Sinadaran Haɗa Bam Ne Ya Fashe A Kano

Published

on

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshin jihar Kano ta ce abinda ya fashe a ranar Alhamis 17 ga watan Mayu, a wani shago a unguwar Sabon Gari da ke birnin wadda ta hallaka mutum tara, ta faru ne a sanadiyyar wasu sinadarai da ake iya haɗa bam da su.

A lokacin da fashewar ta auku an rika yaɗa labarai kan cewa Bam ne ya fashe a wajan.

A yayinda wasu ke cewa tukunyar gas ce ta mai aikin walda ta fashe a shagon.

Amma cikin tattaunawar da yayi da ƴan jarida, a ranar da abin ya auku, Kwamishinan ƴan sanda na Jihar ta Kano, CP Sama’ila Dikko, ya ce tukunyar gas da ake walda da ita a wajen ce ta fashe, “amma ba bam ne ya tashi ba kamar yadda ake faɗa.”

Bayan gudanar da bincike hukumar ƴan sanda ta fitar da sanarwar ta hannun kakakin ta SP Abdullahi Kiyawa, a ranar Asabar 21 ga watan Mayu, 2022.

Rundunar ta ce mutumin da yake gudanar da haramtaccen kasuwancin na sayar da waɗannan haramtattun sinadarai, waɗanda ake haɗa bam da su, da aka gano, Michael Adejo, ya mutu a fashewar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: