Wasu Mutanen da Gwamna Abdullahi Umaru Ganduje ya sa aka yi wa aikin ciwon ido kyauta a unguwar Gama da ke Kano bayan an ɗage zaben gwamna a ranar 9 ga watan Maris, sun makance, wasunsu kuma ciwon idon ya karu.
Wani magidanci, Malam Yusufa, wanda ke yan tsire layin Baba Mai Kwari a nan Gama, ya shaida wa wakilin Muryar Yanci cewa, a da idonsa yana gani, amma bayan an yi masa aiki a wani asibiti mai suna Asibitin Isa Kaita da ke nan dai unguwar ta Gama, sai ya daina gani baki daya.
Hajiya Amina mai ice tabbatar da “Dama ba na gani da idon, to a wannan lokaci da aka ce ga masu aiki sun zo, sai muka tafi wurinsu aka yi min aiki a idon. Aka ce sai bayan mako biyu mu dawo. Tun kafin cikar lokacin idon ya fara azabtar da ni. Da lokacin ya yi muka koma, sai aka ce ai masu aikin ba sa nan sai dai mu koma Asibitin Murtala. Muka je can, likita ya duba ni, ya ce ai ido ya kassara gaba daya. To ni dai yanzu ba ma ta idon nake yi ba, na hakura da shi, amma wannan radadin da ke damuna shi ne nake so ya daina.”
Malama Binta Audu dan Lamido, ta ce a da ba ta gani, amma bayan an yi aiki a idon nata sai ta fara gani. Amma kuma sai idon ya fara ciwo daga baya. Ta ce idon yana mata ciwo yana kuma zubar ruwa. Ta kara cewa wasu cikinsu sun ci nasara idanuwansu ya gyaru, wasu kuma dai abin ya ta’azzara sosai.
Babbar matsalar da masu ciwon idon ke fuskanta, ita ce rashin sanin inda wadanda suka yi mu su aikin suke a halin yanzu. Gashi talakawa ne, ba za su iya zuwa manyan asibitocin kudi ba. Da a ce sun sani, kila su samu sauki tunda su ne suka fara sa hannu a kai, suna da tarihin ciwukan.
Yan unguwar ta gama sun samu tagomashin aikin Titi da kuma na warkar da masu larurar Ido tun bayan da aka ambata cewa zabe bai kammala ba na jihar kano,
Sai gashi lamarin ya bar baya da kura.
Madogara, Muryar yanci