Daga Abba Anwar

Labarin kanzon kurege da Jaridar nan mai adawa da gwamnatin jihar Kano, wato Daily Nigerian ta fito da shi cewar wai kotu ta sauke sababbin sarakunan da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada bisa doka kwanan nan, ba haka ba ne.

Kawai dai a na son a kara kawo rudani ne a wannan cigaba da a ka samu a jihar Kano. Kuma ai ita waccan jarida dama kowa ma ya san irin kallon da ta ke wa wannan gwamnati ta mu. Wajen yarfe da kage da fadar abinda bai tabbata ba a kan wannan gwamnati.

Wani abin lura kuma shine yadda waccan jarida ta yi kaurin suna wajen adawa ta ba gaira ba dalili ga gwamna Ganduje da gwamnatinsa. Wannan labarin wai na sauke Sarakunan Bichi da Rano da Gaya da Karaye, ba haka zancen ya ke ba sam.

Ita waccan babbar kotun ta jihar Kano da ke zamanta a Ungogo karkashin Mai Sharia Nasiru Saminu, cewa kawai ta yi, kowa ya je ya koma a matsayin da ya ke.

To mu a jihar Kano tun daga lokacin da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano ta kawo Kudurin Doka wacce Gwamna Ganduje ya sa wa hannu ta zama Doka, zuwa lokacin da a ka ba wa wadannan sababbin sarakuna takardar shaida musu na wannan zabe da a ka yi musu har zuwa lokacin da a ka ba su sandar mulki, gwamnan Kano bai karbi wata Oda daga kotu cewar ya tsayar da yin hakan ba.

Shi Mai Shari’ah ya bayar da cewar kowa ya tsaya matsayinsa har sai lokacin da za a fara sauraren wancan koke da a ka kai masa. Wanda a ka sa ranar 21 ga Watan Yuni, 2019, mai zuwa. Mu kuma a matsayin da muke shine mun nada wadancan sarakuna masu daraja ta daya. Tun ma kafin a ce wai an ba gwamna wata Oda sabanin hakan.

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano

Leave a Reply

%d bloggers like this: