Wazirin bauchi Alhaji Muhammad Bello Kirfi ya bayyana cewa rashin yin ayyukan cigaban al’umma ne ya sanya su kayar da gwamna maici a zaben gwamnan da yaga bata, Alhaji Bello Kirfi ya bayyana cewa babu wani aiki kwakwkwara guda daya da gwmanan na Bauchi yayi a tsawon shekaru hudun da ya shafe yana mulki a jihar saboda haka ne suka hada karfi da karfe suka kayar dashi a kokarinsa na neman zagaye na biyu na mulkin jihar.
Alhaji Bello Kirfi yayi wannan jawabine a jiya Asabar a yayin taron kungiyar lakcar watan Ramadan akan Gurbacewar Tarbiyya Acikin Al’umma da kungiyar Inuwar Musulmin Nigeria ta shirya a dakin taro na Muhammad Tukur dake tsohuwar jami’ar Bayero, inda yace siyasar Bauchi babu rigingimu da sara suka acikinta, a saboda hakane suka iya kayar da gwamna mai ci ba tare da anyi rigingimu ba sabanin abinda ya faru a zaben Kano.