A karon farko ɗan takarar gwamnan jihar Kano a jam iyyar PDP Abba Kabir ya bayyana cewar ɓarnar kuɗi ne ya sa gwamnatin Kano ta ƙirƙiri sarakuna huɗu a Kano.
Abba Kabir ya bayyana hakan ne yayin shan ruwa da masu hada hadar sufuri a jihar Kano.
Ya ce maimakon gwamnati ta mayar da hankali wajen samar da abubuwan more rayuwa ga al umma amma ta ƙirƙiri masarautu na yadda za ta wawashe kuɗin al umma.
Cikin wata sanarwa mai ƙunshe da sa hannun kakakin ɗan takarar gwamnan Sunusi Bature ya aikewa nujallar Matashiya, ya ce, abinda ya kamata a yi shi ne samar da asibitoci, makarantu da sauran abubuwan da al umma za su amfana.
Amma ba da jimawa ba jama ar Kano za su dara ganin kotu ta kusa kammala shari a a kan zaɓen a cewarsa.
Alhakin rubutu Mujallar Matashiya.