Binciken masana ya tabbatar da cewa rintsawa da rana na rage hawan jini a jikin bil adama.

Binciken wanda babban likita a asibitin Asklepienion da ke Gress ya tabbatar ya ce baccin ya fi amfani ga mutanen da suka kai shekaru 60 ko sama da haka.
Likitan mai suna Manolis Kallistratos ya ce hatta matasa ma na da buƙatar baccin don inganta lafiyar gudanar jininsu.

Cikin gwajin da aka yi na masu ɗauke da cutar hawan jini da ya kai 212 ya ragu zuwa 120 sakamakon baccin na rana kaɗai.

Wata ƙungiyar da ke rajin kula da masu ciwon hawan jini da bugun zuciya da ke ƙasar amurka sun tabbatar da gwajin tare da umartar marasa lafiyan da fara baccin rana don yin adabo da larurar da ke damunsu.
Haƙƙin mallaka Mujallar Matashiya.