Daga Jamilu Lawan Muhammad

Wanda ake zargi mai shekaru 32  a duniya ya sace katinan zarar kudin wanda yake amfani da su idan ya je wajen na urar cirar kuɗi ga mutanen da suka kasance basu da ilimin hakan.

Ya ce yana amfani da katin nasa ne da zummar zai taimakawa wanda ba su iya cirar kuɗin ba sai ya musanya musu da wani daban.

An cika hannu da wannan mutumi ne dai a Jihar Benue, Sunday Onovo, wanda ya fito daga yammacin karamar hukumar Nkanu dake Jahar Enugu mazaunin cikin garin Makurdi.

Shugabar ufishin EFCC dake yankin Makurdi, Nwanyinma Okeanu, ta bayyanawa yan jarida cewar wanda ake zargi an kama shi da daya daga cikin sabon katin bankunan da ke karamar hukumar Otukpo.
Okeanu ta ce wanda ake zargi da yin zamba cikin aminci ya shiga Jami’ar Jihar dake Benue (BSU).

Wanda ake zargin ya ce yana satar kuɗaɗen da suka kai miliyan ɗaya ko sama da haka a cikin jerin mutanen da ya tarar wajen cirar kiɗin

Hukumar ta ce za ta miƙa wanda ake zargin gaban kotu don girbar abinda ya shuka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: