Tare da; Abdurrahman Ibrahim Zage

Dukkan yabo da jinjina sun tabbata ga Allah (SWA), tsira da amincinsa su k’ara tabbata ga babban masoyinsa Annabi Muhammad (S) da alayensa da sahabbansa da wad’anda suka bi tafarkinsu da kyautatawa har zuwa tashin k’iyama.
Daren lailtul k’adri shi ne mafi falalar dararen da Allah ya halitta, saboda tarin ni’imomi, albarka da rahama da ya kimsa a cikinsa.
Dare ne da yake dai-dai da dararen watanni dubu, wad’anda babu wannan daren a cikinsu. Ladan ibada a cikinsa tana dai-dai da ladan ibada na shekaru 83.
Yin ibada a cikin wannan dare guda daya ya fi alkhairi a kan yin ibadar kwanaki 29,530.
Yin ibada a wannan dare kwaya daya ya fi alkhairi sama da yin ibada na sa’o’i (hours) 708,720.
Yin ibada a cikin wannan dare guda daya ya fi alkhairi a kan ibada na dak’ik’ok’i (secons) 42,523, 200.
Daren lailatul k’adri yana da sa’o’i 12, yin ibada a kowacce sa’a daya ta sa ya fi alkhairi a kan ibadar sa’o’i 59,060. wato dai-dai da ibadar shekaru bakwai kenan.
Ma’ana da za ka yi sallah ko zikiri na awa daya a wannan daren, alkhairin sa ya fi ka yi shekaru bakwai kana sallah kana zikiri a jere ba tare da ka tsaya ba.
Haka zalika yin ibada na secon daya a cikin Wannan daren na lailatul k’adri alkhairin sa ya fi na ibadar kwanaki arba’in, dare da rana ba tare an tsaya ba.
Tsarki ya tabbata ga Allah!
An kira shi da lailatul k’adri saboda girman daraja da martabarsa a gurin Allah, a cikinsa ne Allah yake kaddara al’amuran bayi na shekarar dake fuskantowa. Allah Ta’ala ya ce; “Lallai mun saukar da shi (Qur’ani) a cikin wani dare mai albarka, lallai mu mun kasance masu gargadi. A cikinsa (daren) ake rarrabe dukkan al’amura ababen hukuntawa) {Addukkan:3-4}.
Hadisi daga Anas Bin Malik (R) ya ce: ” aiki a daren lailatul k’adri da sadaka, sallah da zakka sun fi girman falala a kan yin su a wasu dararen watanni dubu” {Addurarul manthur: 6:370}.
Don haka da taimakon Allah, za mu yi magana ne dangane da falalar wannan dare mai albarka, bisa hasken ingantattun hunjoji daga taskar Annabta.

*FALALAR LAILATUL K’ADRI:
1-Saukar da Alk’ur’ani a cikinsa, kamar yadda Allah Ta’ala ya fad’a: ” Lallai mun saukar da shi (Alk’ur’ani) a daren lailatul k’adri ” {Suratul k’adri}.

Imam Hakim da waninsa sun rawaito hadisi daga Abdullahi Bin Abbas (R) ya ce; “an saukar da Alkur’ani a dunkule zuwa ga saman duniya ( wani guri da ake kira baitul izzi) a daren lailatul k’adri, sannan bayan haka aka dinga saukar da shi (kad’an kad’an) a tsawon shekaru ashirin”.
2- ladan ibada a wannan daren ya fifici na dararen watanni dubu. Allah Ta’ala ya ce; ” lailatul k’adri ya fifici (dararen) watanni dubu ” {Ak’adri:3}
Sahabi Anas Bin Malik ya rawaito daga Annabi (S) ya ce: ” lallai wannan watan ya fuskanto ku, akwai wani dare a cikinsa da ya ya fifici (dararen) watanni dubu, wanda aka haramta masa shi, hakika an haramta masa alkhairi duka, kuma ba a haramta alkhairi sai ga abin haramtawa” {Ibn Majah:1341}.
3- Saukar Mala’iku a wannan dare mai albarka, domin kewaye muminai a yayinda suke ibada, saboda fadin Allah Ta’ala; “Mala’iku da Arruhu (Jibril) suna sauka a cikin sa da izinin Ubangijin su” {Alkadri:4}
Al’imam Ibn Kathir (R) a k’arak’ashin tafsirin Wannan aya yake cewa: Mala’iku suna yawaita sauka a wannan daren ne saboda yawan albarkarsa, Mala’ikun suna saukowa tare da albarka da rahama, kamar yadda suke sauka a lokacin da ake tilawar Alk’ur’ani ” {Tafsiru Ibn Kathir: 532}.
4- Allah Ta’ala yana gafarta dukkan zunuban bayin da suka tsaya a wannan dare, suna masu imani da neman lada a gurinsa. Annabi (S) ya ce: “wanda ya azumci Ramadan yana mai imani da neman lada za a gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa Kuma duk wanda ya tsaya a daren lailatul k’adri yana mai imani da neman lada a gurin Allah za a gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa” {Sunan Annisa’i: 2201}.
5- Allah Ta’ala yana cika daren lailatul k’adri da aminci da nutsuwa. Da nassin Alk’ur’ani; “aminci ne shi har zuwa hudowar alfijr” {alkadr: 5} .

Tsarki ya tabbata ga Allah! Wanne alkhairi ne ya fi wannan a rayuwar mumini?
Allah ka ni’imta mu da dacewa da wannan dare da kake bonanzar rahama da jin kanka!!

Leave a Reply

%d bloggers like this: