Bayan ajiye aiki cikin yanayin kammala aikin gwamnati kamar yadda gwamnatin ta tsara da Kwamishina Mohammed Wakili (Singam) ya yi, an kawo sabon kwashinan ƴan sanda Ahmed Ilyasu don maye gurbinsa.

Kwamishinan ƴan sanda Mohammed Wakili ya ajiye aikinsa ne a ranar 26 ga watan da muke ciki bayan da ya cika shekaru 36 yana aikin ɗan sanda.

Rahotanni na nuni da cewa sabon kwamishinan ƴan sandan da aka kawo ya kasance yana da matakin Mastarin Digiri a harkokin kasuwanci ta bunƙasa shi.

Tsohon kwamishinan ƴan sanda Mohammed Wakili dai ya yi ƙaurin suna wajen yaƙi da kwaya da maau kwaya kamar yadda a kowanme lokaci ya ke iƙirari

Ko wanne ɓangaren sabon kwamishinan ƴan sanda na yanzu zai fi mayar da hankali?

Akwai ɓangarorii da dama na harkokin tsaro da ke barazana a jihar Kano.

Mujallar Matashiya ta yi nazarin yadda ake amfani da ƴan sanda wajen kauda kai ko aikata laifi da ma basu na goro a mataayin toahiyar baki.

Wannan dai ba sabon abu bane ganin cewa an saɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa

Na biyu jihar Kano babban gari ne da ke ɗauke da miliyoyin mutane, sai dai akwai ƴan sara suka da ke neman zama ruwan dare kamar yadda wasu ke amfani da manyan taruka don yin fashi da taakar rana.

Na uku cin zarafin al umma, wasu daga cikin ɓata garin ƴan sanda na cin zarafin al umma don biyan buƙatarsu musamman idan suka nemi a musu adalci a lokuta da dama, misalin bayar da beli wanda aka ce kyauta ne a kowanne caji ofis ɗin ƴan sanda.

Na huɗu, tsaron lafiya da dukiyar al umma a haka aka gina aikin ɗan sanda amma wasu mutanen na cikin barazana kamar yadda ake safarar miyagun kwayoyi daga wasu ƙasashen zuwa jihar Kano ba tare da tabbatar da hukunta waɗanda ake zargi idan an tabbatar da sun aikata laifi ba.

Na biyar walwalar jama a tare da amsa sunan Ɗan sanda abokin kowa, yadda ƴan sanda za su shigo da sabbin hanyoyi don ƙara ƙulla alaƙa tsakaninsu da mutane na yadda za su saki jiki har su bada bayan sirri ga jami an tsaro ba tare da fargabar watangaririya da rayuwarsu ba.

Mujallar Matashiya ta yi wani hoɓɓasa na yin wani faifan bidiyon yadda za a kawo sauyi a wani ɓangaren na aikin ɗan sanda kamar yadda za ku gani a ƙasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: