Alhamdulillah yau ranar rantsuwar!
Yau dai mun tsallaka next level Ina Taya Mai girma shugaban kasa Muhammad Buhari da Mai girma gwamnan Kano Dr Abdullah Umar Ganduje bisa wannan rana. Ina rokon Allah yasa gaba tafi baya yawan alkhairai domin nidai a fahimtata first level din nan talaka Bai Sami wata riba ta abin azo a gani ba, a Nigeria Koda ma maki za a bayar sai dai muce ba yabo ba fallasa, Ina magana ne akan talaka Wanda a baya yake sayen shinkafa buhu nara dubu 8 yanzu Kuma zamanin Buhari muke Saya dubu 15, kunsan dai farashin man fetur kafin zuwan Mai girma Buhari yanzu Kuma kunsan Ana wa muke samunsa, a takaice dai farashin komai ya tashi a wannan, zamani nawace kujerar Makka a baya Amma yanzu anawa ake zuwa? babu shakka dole mu gayawa Mai girma PMB cewar wallahi yunwa ta karu sosai masu cin abinci sau 3 a rana sun ragu. Musamman a Arewacin Nigeria. Amma duk da yazama dole mu jinjina maka ya mai girma shugaban kasa la ‘Akari da kokarin ka a Fannin Kan abin da yashafi Boko haram, amma kuma an sami sakacin ta’ azzarar kashe kashen mutane a Zamfara da katsina GA masifar garkuwa da mutane wacce ta fantsama a fadin kasar nan. Ya Mai girma PMB nasan watakila kana kokartawa amma mu na kasa bazamu Iya gani ba domin duk kokarin ka idan cikin mu Bai dauka ba idon mu bazai Iya gane komai ba, kasan ance yunwa Bata da hankali Kuma gaskiya ana Fama da yunwa da fatara a Arewacin Nigeria. Wani abu da yakamata Baba Buhari ya duba shine batun ministocin nan har ma da kwamandodin rundunonin tsaro gaskiya lokaci yayi da za a ce ba a tsallaka next level dasu ba, yakamata ayi sabon zubi domin ni a fahimtata ta tsaka tsaki Ina GA basu tabuka komai ba, Musamman namu na nan Arewacin Nigeria wakilcinsu Bai amfana mana komai ba, amma idan akwai me gyara a shirye nake na karbi gyara. Mai girma PMB a tarihin Nigeria tun daga 1999 zuwa yanzu ban taba ganin shugaban da talakawa suka yiwa goma ta arziki kamar ka ba, dan haka nake ganin cewar lokaci yayi da suma zasu Shana a next level, talakawa Kai har da nakasassu masu Bara a titi naga sun sayi katin nan sun kankare sun aika maka saboda a zaton su Kai ne sarkin fiton samar musu da mafita, amma gashi yawanci gwiwowinsu sun yi sanyi jikinsu yayi la’asar wasu gani suke kamar ba Buharin da suka zaba bane watakila ko anyi musu musaya. A karshe nake rokon PMB ya yi tilawar alkawurran da yayi mana kafin zabe Musamman wadanda suka shafi abinci da ilimi da tsaro, domin tabbatar dasu a next level domin a first level din nan an sami matsala. Shifa talakan Nigeria saukin kai Gare shi idan ka bashi abinci da ruwa ka inganta masa harkar lafiya ka gyara kasuwanci da makarantun da zai kai yayansa shikenan ka birge shi. A karshe nake rokon Allah yayi riko da hannun ka ya mai girma PMB Allah ya taimaki Nigeria.
Nasir Zango


