A wannan watan an tattauna batutuwa da dama a shafukan sadarwa na zamani kama daga batun Marriage is not an archiveme da kuma batun Datti Assalafy sai kuma na shari’ar gwamnan jihar Zamfara a karshen watan kuma an samu sabon batu mai zafi biyo bayan wani rubutu da Dr. Sheriff Almuhajir yayi kan jama’ar jihar Kano wanda bai yiwa Kanawa dadi ba, a yanzu dai wannan batu shike ci gaba da bude sabon salo a shafukan sadarwar malam bahaushe.

Sai dai a wani salo da za’a iya kira da ramuwar gayya fitaccen da jaridar nan Nasiru Salisu Zango ya caccaki waccan batu na Almuhajir inda yayi raga-raga da maganganunsa, kuma jama’a da damane suka bayyana ra’ayinsu kan batun a shafin na Zango, kardai na cikaku da sururu karanta cikakken rubutun na Zango a kasa.
“Kano ! ba dai mutum ba sai dai Allah…

Kano garin mu ne kuma bamu da inda ya fi Kano Dan haka babbar godiya ga Allah da yayi mu kanawa a Nigeria.
Na lura kana da sha’awar zagin mu da iyayen mu a duk sanda a tagargajen ka ta motsa maka, to lokaci yayi da zamu gaya maka cewar shirun mu da kau da kan mu fa ba tsoro bane kawaici ne Wanda watakila baka sanshi ba.

Na san ba wannan ne Farau ba da kake rubutu ka zagi mutanen Kano ba, amma na lura shirun da ake maka shike kara maka kwarin gwiwar cigaba da cashewa.
Mu dama a Kano haka muka gada mu goya baki mu rungume su mu basu mutsuguni kuma su zage mu mu kyale su domin arziki muka gada. Duk sanda garin Ku yayi maka zafi Kano kake shigowa ka fake, lokacin da yan uwan ka suke tsaka da tashin bama bamai a garuruwan ku, Kano kake zuwa ka sarara, har yanzu Kano tafi garin Ku a gunka amma karfin hali na son a sani yasa baka da abin zagi sai mu da iyayen mu. Kuma matsalar mu a Kano itace yadda muke karbar bako mu karramashi har ya dunga tunanin isarsa ce tasa muke masa, wannan kuwa gado muka yi daga iyayen mu na rashin kyamar baki, shiyasa duk Wanda masifar garin su ta fatattako shi Kano ne wurin zaman sa, dubi yadda yan uwan ka da waccan masifar ta garin Ku ta koro dubi yadda muke basu mafaka saboda abin da muka gada kenan mutum ya zage mu ba bashi gurin kwana.
Allah nagode maka da kayo ni Dan Kano asaliyan. Kuma a shirye nake da kulla yaki da duk Wanda baya son Kano, idan har zaka zage mu kayi zaman ka a garin Ku mana.
Allah ka taimaki Kano da kanawa kuma ka bamu ikon taimakawa bakin haure ko zasu kwana suna surfa mana ashar.