Sabon gwamnan jihar zamfar Bello Muhammad Matawalle ya sadaukar da Albashinsa ga Gidan Marayun jihar zamfara na kowane wata don tabbatar da jin daɗinsu da walwalarsu.
Gwamnan wanda ya lashe zaɓen a inuwar jamiyar PDP ya bayyana hakan ne, a ziyarsa ta farko gidan marayun jihar zamfara tun bayan da aka rantsar dashi.

Gwamna Matawale ya bayyana wa marayun cewa su kwantar da hankulansu za su yi rayuwa tamkar suna gidan iyayansu, kuma duk wani abin jindadi na rayuwa za su same shi a cikin wannan gwamnatin da yardar Allah.
Haka zalika gwamanan ya ɗau alkawarin inganta iliminsu da kuma ba su ayyuka ga wadanda su ka kammala karatu daga cikin su.


Allah yai masa jagora yabashi ikon sauke nauyin alkawari,