Binciken ya ƙara da cewa mafi yawa daga cikin mutanen da ke ta ammali da kayan ƙara kuzari ƴan shekaru 18 ne zuwa 40.

An tabbatar da cewar akwai barazana kamuwa da cutar hawan jini ga mutanen da ke yawan shan kayan da za su ƙara musu kuzari a kai a kai.
Ƙungiyar kula da lafiyar zuciya ta ƙasar amurka ta ce zuciya na cikin hatsarin kamuwa da hawan jini musamman ga mutanen da ke shan kayannƙara kuzari a ƙasa da mituna 20.

Binciken da jami ar Pacific da ke ƙasar Amurka ta yi ta nuna cewar zuciya na iya bugawa lokaci guda wanda hakan na iya sanadiyyar rasa rayuwar ɗan adam.

Mujallar Matashiya ta yi nazarin akwai mutane da dama da ke ta ammali da kayan sha masu ƙara kuzari a Najeriya.
(c) Mujallar Matashiya.