Addini
NA SHA NONON MATATA , YAYA AURANMU
Daga Jamilu Zarewa
Tambaya :
Don Allah malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa, ya aurensu yake ?
Amsa :
To dan’uwa Allah madaukakin sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila, don haka ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa maganganu guda biyu :
1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102, ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure, wannan ita ce maganar mafi yawan malamai .
2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.aw. ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma, wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure .
Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, saidai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau.
Don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67.
Addini
Malam AbdulJabbar Kabara Ya Kori Lauyoyin Sa Ya Buƙaci Kotu Ta Bashi Dama Zai Iya Kare Kansa
Malam Abduljabbar Kabara ya ce ya kori lauyoyinsa saboda sun saɓa yarjejeniyar da suka yi.
Malamin ya bayyanawa kotun haka a yau Alhamis yayin da ake ci gaba da sauraron shari’ar.
A cewar malamin yanzu yana sake neman wasu lauyoyin da zasu tsaya masa.
Wannan shine karo na uku, da Malamin dake tsare a gidan gyara hali, ya sake watsi da Lauyoyinsa.
Malam Abduljabbar kamar yadda ya yiwa Lauyoyinsa na baya, yana zarginsu da gaza kare shi a gaban Kotu.
Su kuwa lauyoyin gwamnatin jihar Kano sun buƙaci kotun ta umurci hukumar dake baiwa marasa ƙarfi kariya a kotu kyauta, watau Legal Aid Council da ta bawa Malamin lauyan.
A ƙarshe, kotun ta amince da hakan kuma ta yi umarni ga Legal Aid Council ta bawa Abduljabar Lauyoyin da za su kare shi.
Sai dai, Malam AbdulJabbar ya buƙaci kotu ta rabu da shi zai iya cigaba da kare kansa, tunda duk lauyan da ya ɗauka sai ya ce ana yi masa barazana da rayuwarsa.
A ƙarshe mai shari’a ya ɗage zaman zuwa ranar 26 ga Mayu, 2022.
Addini
Fasto Dake Sayar Da Aljanna Kan Kuɗi N310000, Ya Gurfana Gaban Mai Shari’a
Ahmad Sulaiman Abdullahi
An gurfanar da Fasto Abraham malamin addini a kotu wanda ya faɗa ma mabiyansa cewa yana iya kai su aljannah, inda yace musu Omuo-Ekiti ne ƙofar shiga aljanna.
Fasto Abraham dai ya nemi mabiyansa su biya kuɗi N310,000 domin shiga aljannah bayan ya ce masu ya san hanyar da ake bi a shige ta.
An gurfanar da faston a wata kotun majistare ta jihar Ekiti da ke zama a Ado-Ekiti.
Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Johnson Okunade, ya ce laifin ya saɓa wa sashe na 416 na dokar laifuka ta jihar Ekiti na shekarar 2012.
Johnson ya ƙara da cewa kai Fasto Noah Abraham Adelegan a ranar 27 ga watan Afrilu, a Omuo Oke-Ekiti a yankin Omuo, ta hanyar karya da niyar zamba, ka gabatar da kanka ga taron jama’a a cocin Christ High Commission Ministry, Omuo, Oke-Ekiti, a matsayin wanda zai iya kaisu aljannah kafin tashin duniya.
Inda nan take suka biya kuɗi daga N300,000 zuwa N310,000 kwannensu.”
Lauyan wanda ake ƙara, Adunni Olanipekun, ya buƙaci kotun da ta bayar da belin wanda yake karewa, inda ya ƙara da cewa a shirye yake ya gabatar da amintattun wadanda za su tsaya masa.
Sufeto Okunade yace bashi da ja akan buƙatar belin, amma ya buƙaci kotun da ta yi amfani da damar ta wajen bayar da belin ko kuma ƙin amincewa da shi.
Alkalin kotun mai shari’a Titilola Olaolorun ta bayar da belin wanda ake ƙara a kan kudi N100,000 tare da mutane biyu da za su tsaya masa.
A ƙarshe mai shari’ar ta ɗage sauraron karar zuwa ranar 24 ga watan Mayu.
Addini
Hisbah A Kano Ta Cafke Ƴan Mata Takwas A Wajen Raƙashewa
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sami nasarar kama wasu mata masu ƙananan shekaru a rukunin unguwar Nassarawa ta jihar.
Mai magana da yawun hukumar Lawal Ibrahim Fagge ya tabbatarwa da Matashiya TV cewar, an kama ƴan matan ne a wuraren hokewa kamar Pikolo Joint da wani gida mai suna ICU da ke unguwar Badawa a Kano.
Hukumar ta kai sumamen ne bayan samun rahooto a kan yadda ake samun ɓata gari na ta’ammali da miyagun kwayoyi da shan shisha da sauran ayyukan ashsha a wajen.
Babban kwamandan hukumar Ustaz Haroon Ibn Sina ya ja hankalin iyaye da su dinga kula da ƴaƴansu tare da tunatar da su a kan haƙkin da ya rataya a wuyansu na kula da tarbiyya.
Sa’annan ya aike da takardar gayyata ga iyayen ƴan matan da aka kama don ganin sun zo domin tantance yaran da aka kama.
Hukumar Hisbah ta ce ba za ta lamunci yadda wasu ɓata gari ke gudanar da ayyukan ashsha a jihar ba, kuma za ta sa ƙafar wando ɗaya da duk wanda ya yi ƙokarin tsallake dokokin ta.
-
Labarai10 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari