Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da hawan nassarawa a kano.

Hawan da ake yi duk shekara bisa al adar masarauta.
Cikin sanarwar da ofishin sakataren gwamnatin ta fitar ta bada sanarwar cewa gwamna ba zai sami damar halartar hawan daushe ba, haka kuma ba za a samu damar gudanar da hawan nassarawa ba saboda wasu dalilai.

Tun tuni dai a raba hawan nassarawan biyu, wanda kuma daga baya gwamnatin ta bada sanarwar dakatar da hawan baki ɗaya.

Dambarwar tsakanin gwamna Ganduje da Sarkin Kano Muhammad Sanusi ll dai ta fara ne tun bayan da aka kammala zaɓen gwamna har ma aka ƙirƙiri sabbin masarautu huɗu a jihar.
(C) Mujallar Matashiya