Binciken ya tabbatar da cewar ko da mutanen da ke kallon fim ɗin mage tunaninsu ya zarce na sauran jama a da ba sa mu amala da magen.

Wani bincike da jami ar American University suka yi ya tabbatar da cewar mutanen da ke kiwon mage sun zarce sauran mutane basira da kuma zurfin tunani.

Mage na da tsawon rai da ta ke kai shekaru 10 zuwa sama.

Kuma ko da wajen renon ƴaƴanta tare da tarbiyyarsu ba daidai yake da na sauran dabbobi ba, tana yin nata kamar na mutane.

Mista Clinton wanda ya jagoranci binciken mai zurfi wanda aka ɗauki tsawon shekaru 13 ana yi ya ce matuƙar mutum na kiwon mage zai kara samun kuzari da lafiya a jikinsa.

A binciken wanda ya bada tabbacin cewar mage jinsin dabba ce ta daban wadda ke nuni da cewar babu wani abu da za ta gani zai cutar da mai ita ba tare da ta yi iya bakin ƙoƙarinta ba.

Jinsin dabba na mage dai na da shiga rai tare da yin mu amala da mutane tamkar mutanen a wasu lokutan wanda har ta kai bayan ranar mage da wasu ƙasashen suka ware wasu mutaanen na sadaukar da duk abinda suka mallaka ga magen tasu.

Mujallar Matashiya ta gano yadda mutane ke sakin jiki da mage ba kamar sauran dabbobi ba ko a Najeriya.

(C) Mujallar Matashiya

Leave a Reply

%d bloggers like this: