Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano ya yi holen masu garkuwa da mutane da ƴan fashi da makami, ɓarayi da ƴan daba.

An yi holen masu garkuwa da mutane su fiye da 140 ciki har da masu satar ababen hawa da ƴan sara suka.

Tun da fari dai kwamishinan ya sha alwashin fatattakar masu aikata laifuka a faɗin jihar tun bayan fara aikinsa a Kano.

An yi holen mutanen ne a helkwatar rundunar ƴansanda ta jihar Kano da ke Bompai.