A wasan sada zumunta da aka gudanar yau a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, ƙungiyar kwallon ƙafa ta Kano Junior Pillars ta lallasa Kannywood da ci 6-2.


Wasan da aka gudanar da shi a yammacin yau, wakilin mujallar Matashiya Idris Ya’u ya bamu labarin cewa, an gudanar da wasan lafiya an tashi lafiya.
An yi wasan ne don sada zumunta a lokacin shagalin bikin sallah ƙarama, wasu daga cikin waɗaɓda suka buga wasan a ɓangaren Kannywood sun bayyana cewa, wasan ya basu ƙafa dalilin da ya sa aka yi musu warwas.

Idan ba a manta ba a wasan da aka gudanar tsakanin Kano Pillars da Kannywood shekarun baya ƙungiyar Kano Pillars ta lallasa Kannywood da ci fiye da goma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: