Kamar yadda wuta ke ƙara ruruwa yayin da dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi, an yi wani zaman sirri tsakanin gwamnan da sarkin da kuma wasu manya a kasar nan.

cikin zaman wanda aka yi a Abuja Alhaji Aliko Ɗangote da shugaban ƙungiyar gwamnoni Kayode Fayemi na daga cikin mutanen da suka jagoranci zaman.
Yayin zaman dai Sarkin Kano ya taya gwamnan jihar Abdullahi Ganduje murnar sake lashe zaɓen sa a karo na biyu.

Haka kuma an cimma matsayar yarjejeniyar cigaba da aiki tare bayan da aka sulhunta su.

Sarkin Kano wanda ya samu rakiyar wasu daga cikin ƴan masarautar.