Shugaban ƙungiyar Mabiya Addinin Kirista (CAN) A jihar ta kaduna Joseph Hayab ya buƙaci gwamnan jihar Nasir EL Rufa’I da kar ya kuskura ya sa hannu a dokar bada lasisin wa’azi a jihar.

Hayab yace suna nan suna nazari akan dokar sannan kuma zasu ɗauki matakin shari’a kan majalisar dokokin Muddin basu gamsu da dokar ba.
Sai dai anata ɓangaren jama’atul Nasril Islam, tayi maraba da dokar ta hannun sakatarenta Yusuf Adamu.

Tun makon da ya gabata ne majalisar jihar kaduna take ƙoƙarin samar da dokar hana yin wa’azi a jihar har sai an an bada lasisi tare da tantance irin wa’azin da za’ayi.
