A gobe talata ne hukumar shirya jarabawa shiga jami’a wato JAMB zata gudanar da taro tare da masu faɗa a fannin ilimi, don tsayar da matsaya kan mafi ƙarancin Makin da zai baiwa dalibai damar shiga jami’a.

Babban jami’in yaɗa labarai na hukumar Fabian Benjamin ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Abuja.

Benjamin ya bayyana cewa a goben za’a tsayar da matsaya kan makin da ake buƙata na shekarar 2019/2020 A bainar jama’a.

Ya kuma yi kira ga ɗaliban da suyi watsi da duk wata jita- jita da ake yaɗawa kan makin da hukumar zata fitar. A cewarsa su bari sai an kamala fidda matsaya sannan zasu ji a hukumance.