Shugaban  ƙasa Muhammad Buhari  ya nuna damuwarsa matuƙa kan kisan aƙalla mutane 25, a yayin wani mummunan hari da aka kai ƙaramar hukumar Rabah dake jihar sokoto.

A wata sanarwar da mataimakinsa kan kafafen yaɗa labarai  malam Garba shehu ya a Abuja yana mai cewa an sanar da Muhammad Buhari lamarin inda ya miƙa ta’aziyar sag a gwamanan jihar sokoto Aminu waziri Tambuwal, da iyalan matatan, da al’ummar jihar baki ɗaya.

Sai dai rahotannin da muka samu a halin yanzu, dai tuni jami’an tsaro suka chafke masu hannu akan hare haren inda shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa bazata lamunci ayyukan ta’addanci ba da kuma kisan mutanen da basu ji basu gani ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: