Ƴan hamayya da gwamnatin ƙasar sudan sunyi kira da mai’akatan ƙasar dasu shiga yajin aikin gama gari don tilasatawa majalisar sojin ƙasar Miƙa mulki ga fararen Hula.

Tun bayan da sojiji suka buɗe wuta akan masu zanga- zanga a Khartoum babban birnin sudan.
Haka zalika kuma rahotanni na nuni da cewa jami’an tsaro sun kame wasu tsoffin ƴan tawayen ƙasa da kuma jagororin masu hamayya da gwamnati.

A baya dai Frayiministan Habasha Abiy Ahmad yaje ƙasar don sasanta tsakanin sojoji masu mulki da kuma masu zanga- zanga kin mulkin sojojin sai dai abin yaci Tira.
