GWAMNAN jihar kano Abdullahi Umar Ganduje ya fito da sabbin tsare tsaren harkokin tsaro a faɗin jihar, ta hanyar amfani da ƴan sandan da kuma sabon tsarin da ake amfani da shi a duniya na amfani da mutane yan sa kai dake masarautu biyar a jihar nan,

Inda ya bayyanatsarin zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a faɗin jihar dam aba Najeriya baki ɗaya.
Cikin wata sanarwar da sakataren ƴada labarai na gwamnan Abba Anwar ya fitar cewa gwamna Ganduje ya himmatu wajen magance matsalar tsaro a faɗin jihar.

Gwamnan ya kuma umarci sarakunan jihar guda biyar dasu cigaba da gudanar da taro na wata-wata da zasu dinga maida hankali kan matsalar tsaro a jihar.
