An dakatar da Neymar daga yin duk wani kwantaragi na wayar da kai da kuma yin talluka, biyo bayan zargin da ake masa nay i wa wata mata fyaɗe , sai dai jaridar NR Ta musanta zargin da ake wa Neymar ɗin.

Zargin dai ya biyo bayan wata mata ƴar ƙasar Brazil mai shekaru 27 ta bayyana cewa Neymar yayi mata fyaɗe a wani Otal dake Birnin Paris.
Zuwa yanzu dai ƴan sandar birnin Sao Paulo na cigaba da bincike kan zargin da ake wa Neymar.

Haka zalika matar ta bayyanawa masu binciken cewa sun haɗu da Neymar ɗin a shafin sada zumunta na Instagram inda ya biya mata kuɗin jirgi tare da kama mata ɗaki a Otal.
