Gwamnatin tarayya ta ware gobe laraba a matsayin hutu ga ma’aikatu a faɗin Najeriya kasancewar gobe 12 gawata shine rana Dimokaraɗiya a Najeriya.

Wannan sanarwar ta fito ne a ƙunshin jawabin da ministan cikin gida Abdurahman Danbazau ya sanya wa hannu, ta bakin kakakin hukumar Muhammad Manga.
Inda yace rana ce da za’a dinga tunawa da ƴan mazan jiya wanda suka bawa ƙasa gudunmawa dan tabbatuwar Demokaraɗiya,
Sannan kuma a cika da yiwa ƙasa addu’in zaman lafiya da samun nasara a dukkanin al’amuran cigaba.
A jiya ne dai Shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya sanya hannu dokar chanza ranar demokaraɗiya daga ranar 29 May zuwa 12 june.

