Babbar Jamiyar hamayya ta PDP ta fitar da sanarwa a zaɓi Senator Ali Ndume, a matsayin shugaban majalisar dattijai da kuma Hon Umar Muhammad Bago a matsayin shugaban majalisar wakilai, bayan rantsar da majalisar ta tara a yau talata.
Sanarwar ya fito ne a yau talata ta bakin sakataren majalisar ta PDP Umar Ibrahim Tsauri, inda ya tabbatar da jamiyar PDP tana goyon bayan Ndume da Umar Bago, haka kuma tana umartar Ƴan jamiyar da,su mara musu baya a majalisun biyu don ganin sun zama shuwagabannin majalisun biyu.

A ɓangare guda jam’iyar APC mai mulki ta tabbatar da goyon bayan senator Ahmad Lawal a matsayin shugaban majalisar dattawa, da kuma Femi Bjamiala a matsayin shugaban majalisar wakilai zango ta 9.

