Hukumar kula da shirya gasar firimiya ta kasa NPFL ta ci tarar Kano Pillars milyan takwas sakamakon abun da takira rashin da’a da magoya bayan kungiyar sukayi a wasan da suka tashi daya da daya da kungiyar kwallon kafa ta Enugu Rangersa a legas ranar lahadi da ta gabata.
Haka kuma hukumar ta ta ce Pillars za ta yi wasa uku ba tare da magoya baya nan gaba haka kuma hukumar ta dakatar da kaftin na kungiyar Rabiu Ali daga buga wasa har guda goma sha biyu saboda samunsa da lefi lokacin da hatsaniyar ta faru a wasan.
Daga bangaran kungiyar ta Pillars kuwa tuni ta barranta kanta da faruwar lamarin inda ta bakin mai magana da yawun ta Lirwanu Malika Garu ya bayyana cewa ba magoya bayan Pillars bane sannan sabo da haka ne suka janye aniyarsu ta zuwa da magoya baya kallon wasan karshe da aka buga a birnin na Lagos.
Bayan yanke wannan Hukunci kungiyar ta bayyana cewa zata daukaka kara don samun adalci a gaba sannan yayi kira ga magoya bayan kungiyar dasu zauna lafiya a ko’ina suke.
Idan ba a manta ba samun hatsaniya a wasanni a Najeriya ba sabon abu bane lamari da ake dangantawa da son zuciya da ake ganin alkalan wasa sunayi wanda hakanne kesa ana yawan samun rikici a wasanni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: