A hukumar HISBAH an samu raguwar shigar da korafe karafe kamar yadda a yau dinnan hukumar tayi tsit babu wani karafi da muka ci karo da shi.

Wanda faruwar hakan take nuni da aikata ayyukan laifi sun samu raguwa, majiyar Mu ta bamu labarin a yau jami an da ke kula da shigar korafe korafe suna zaune a ofisoshin.
Mutanen da ke harabar hukumar a yau yawancin su masu karbar kudin ciyarwar yayan sune yawancinsu wadanda suka rabu da mazajen sune suke kula da rainon yayan su wadanda suke bin bashin kudin ciyarwa, walau an ajiye azumi basu samu abubuwan bukat daga tsofaffin mazajen su.

Idan za,a IYA tunawa hukumar HISBAH tun kafuwar ta take bayar da gudummawa ta fuskar karbarwa marasa galihu hakkinsu, dan haka ne yasa hukumar ta dauki gabaren karbarwa matan da suka rabu da mazajen su hakkin yayansu kanana wanda ya shafi ciyarwarsu da tufatarwarsu da sauran hakkokin Yaya akan iyayen su.
