Ƴan sandan jihar Oyo sun ceto Aƙalla mutane 20 daga hannun wani da ake zargin cewa matsafi ne shi.
Wanda ake zargin mai suna Alfa Oloore da ke unguwar Agungun, a garin Ibadan, Jihar Oyo.
Ƴansandan sun samu rahoton sirri ne ba bakin Al’ummar unguwar Agungun.

Anyi nasarar ceto mutanen da matsafin ya killace su a gidansa duk sun rame sun bushe tamkar ƙwarangwal.
Tuni dai ƴan sandan suka sami nasarar kama shi, suna kuma tsare da shi domin amsa tambayoyi.
A cewar wasu mazauna unguwar, Alfa Oloore, wanda yake nuna cewa shi mai bayar da maganin gargajiya ne, ya kwashe shekaru masu yawa yana gudanar da wannan aikin tsafi, wacce aka jima ana shayin hanashi.

Gbenga Fadeyi, shine kakakin ƴansandan (PPRO) ta jihar ya tabbatar da kama Alfa Oloore sannan kuma wanda aka ceto a halin yanzu suna asibiti don karɓar magani da kulawa ta musamman don ceto rayukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: