A safiyar yau Juma’a ne aka sake gurfanar da matashin nan da ya kai hari massalacin juma’a A ƙasar New Zealand tare da hallaka mutane 50 a gaban kotu.

Sai dai Yaƙi amsa laifin nasa inda ya musanta zargin duk da a baya ya amince.

Maharin mai suna Brenton Tarrant ɗan shekaru 28 wanda ya kai harin a wani masallacin juma’a a watan Maris, tare da hallaka mutane 50 da dama kuma suka jikkata.

A baya dai kafin ya kai harin sai da ya sanar da Friminstan ƙasar cewa zai kai hari sai dai kafin a ɗau mataki ya riga ya kai harin.
Zuwa yanzu dai yaƙi amsa laifinsa a gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: