Sabon labari: Wani malamin makaranta ya rataye kansa a Kano

Shi dai wannan al’amari ya faru ne a yau jumu’a a unguwar Dakata dake nan Kano inda wani mutum mai shekaru 40 a duniya mai suna Femi Oguntumi malami a makarantar Karish College dake unguwar Kawaji, dan asalin jihar Ondo ya rataye kansa a daki wanda hakan yayi sanadiyyar rasa ransa har lahira.

Wani da suke zaune a gida daya da marigayin ya shaidawa wakilinmu Rabi’u Sani Hassan cewa wani abokin Femi ne yazo yake cigiyar abokin nasa kasancewar yau basu hadu ba kuma ya kira wayarsa bata shiga inda a karshe aka bude kofar dakinsa inda aka tsinci gawarsa aciki har ta fara wari.
Har izuwa yanzu dai ba’a kai ga gano musabbabin da ya sanya shi aikata wannan danyan aiki ba, sai dai abokansa sunce yayi fama da rashin lafiya a kwanakin baya.

A nasa bangaren kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da wakilinmu Basheer Sharfadi faruwar wannan al’amari inda yace tuni suka dauki gawar marigayin suka garzaya da ita zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed sannan kuma tuni kwamishinan ‘yan sanda na jiha ya bada umarnin tsananta bincike akai.

Kalli hotunan yadda marigayin ya rataye ransa:


Allah ya kyauta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: