A yau juma’a 14 ga watan yuni shine ya cika kwana 43 dai dai da sace magajin Garin Daura Musa Umar Uba.

Tun 1 ga watan mayu ne aka sace magajin garin a gaban gidansa inda har yanzu ba’a san ko su waye suka sace shi ba.

Sai dai Rundunar ƴansandan jihar sun bayyana cewa suna iya ƙoƙarinsa don ganin sun ceto shi daga hannun Waƴanda suka yi garkuwa dashi ba duk da har yanzu basuji daga bakinsu ba.
Kamar yadda kakakin Ƴansandan jihar katsina SP Gambo Isa ya bayyana.

Ɗan Lawal ɗin Daura Umar Umar Ata ƙani ne ga magajin daura ya bayyanawa manema labarai cewa tun da aka sace shi har yanzu basuji daga gareshi ba balle masu garkuwan dashi.

Magajin Daura dai ƙani ne ga Sarkin Daura Farouk Umar Farouk, kuma sirikin shugaban ƙasa ne Muhammad Buhari kasancewar yana Auren Hajiya Bilki ƴa ce ga yayan shugaban ƙasa.
Haka zalika shima tsohon Jami’in Kwastam ne.

Leave a Reply

%d bloggers like this: