Gwamnatin jihar Adamawa ta tabbatar da ɓullar annobar amai da gudawa a sassan jihar.
Aƙalla mutane 76 ne aka tabbatar sun kamu da cutar wanda kuma ɗaya daga ciki ya mutu.
Ma’aikatar lafiya ta jihar ce ta tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ɓukaci Al’ummar jihar da su ɗauki matakin tsaftace muhallinsu don gudun yaɗuwar cutar a jihar baki ɗaya.
Haka zalika kuma hukumar ta buƙaci a gaggauta ziyartar asibiti da zarar anji alamun ɓullar cutar.
Annobar dai tafi tsamari ne a yankin ƙaramar hukumar yola ta kudu, da ta Arewa da kuma ƙaramar hukumar Girei.

Leave a Reply

%d bloggers like this: