Babbar kotun tarayya anan kano ta dakatar da gwamnatin jihar kano da hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar kano da su dakatar da duk wani binciken zargi da ake wa masarautar kan almubazzaranci da kuɗi Naira miliyan dubu uku, da miliyan huɗu.

Umarnin ya biyo bayan ƙarar da muhammad Munir Sunusi ɗanburan kano ya shigar kan kotu ta dakatar da gwamnan jihar jihar kano Abdullahi Umar Ganduje, da hukumar ƙarɓar ƙorafe ƙorafe da ma kwamishinan shari’a da da duk wani jami’in gwamnati da ka iya binciken masarautar kano.

Mai sharia Obiala ya bada umarnin da asanar da mutanen da ake ƙarar wannan Umarnin ta hanyar wallafawa a jaridar Daily Trust, tare da miƙa Kofi ga kwamishinan shari’ar jihar kano.

Daga bisani mai sharia ya ɗage zaman zuwan 28 ga watan nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: