Gwamnatin Saudiya ta caccaki rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar da wani Rahoto dake nuni da cewa akwai kwararan shaidu dake nuni da cewa akwai sa hannun Yarima Mohammad Bin Salman a kisan ɗan jarida Jamal Khashoggi.
Rahoton ya kuma buƙaci a hukunta masu hannu a kisan dan jaridar wanda aka yi gunduwa-gunduwa da namansa a ofishin jakadancin Saudiya da ke birnin Santanbul ta ƙasar Turkiya a cikin watan Oktoban 2018.
Sai Gwamnatin saudiya ta musanta wannan zargi da bakin,Karamin Ministan Harkokin Wajen Saudiya, Adel al-Jubeir ya bayyana cewa, babu wani sabon zance a cikin wannan rahoto na Majalisar Dinkin Duniya domin kuwa rahoton na nanata abubuwan da tuni aka yaɗa wa duniya a can baya ne.
Ministan ya ce, rahoton na ɗauke da ruɗani da zarge-zarge marasa tushe, bare makama,wanda ya tabbatar da rashin sahihancin wannan Rahoto.
Sai dai ita ma ƙasar Turkiya ta amince da wannan rahoton na cewa akwai sa hannun Yarima Akan kisar ɗan Asalin Ƙasar wanda yake aiki A fadar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: